1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin rokoki ya kashe sojojin Yemen

Abdul-raheem Hassan
January 7, 2020

Sojojin gwamnati 11 sun mutu sama da 20 sun jikkata a wani sabon harin rokoki da ake zargin 'yan tawayen Houthi suka harba a sansaninsu na Al-Sarain a lardin Ad-Dali a Kudu maso yammacin kasar Yemen.

https://p.dw.com/p/3VrOQ
Jemen al-Dhalea Anschlag auf Militärparade
Hoto: Reuters/Stringer

Wannan hari shi ne karo na biyu cikin mako daya bayan harin farko da ya kashe sojoji biyaar a watan karshen shekarar 2019. Duk da shiga yakin da kasar Saudiyya ta yi a 2015 'yan tawayen Houthi na rike da riko da babban birnin kasar Sanaa da wasu yankun arewacin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya na kwatanta yakin Yemen a matsayin yaki mafi muni da ya gallaza rayuwar fararen hula bayan da yakin ya kashe dubban mutane miliyoyi suka yi gudun hijira.