1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Habasha sun nitse a tekun Yemen

Mouhamadou Awal BalarabeDecember 8, 2014

Rashin kyaun yanayi da kuma cunkosone ya sa jirgin ruwan da ke dauke da 'yan Habasha yin hadari a mashigin ruwan kasar Yemen.

https://p.dw.com/p/1E0dl
Hoto: picture alliance / ROPI

Akalla 'yan Habasha 70 sun nitse a tekun kasar Yemen a yunkurin da suka yi na tsallakawa kasashen da suka ci gaba don kyautata rayuwarsu. Baya ga rashin kyaun yanayi, wannan hadarin ya faru ne sakamakon cika makil da mutane da jirgin ruwan da yake dauke da su ya yi. Ma'aikatar harkokin cikin gida na kasar Yemen ta tabbatar da wannan labarin a cikin wata sanarwa da ta sanya a shafinta na Internet. Sai dai ba ta bayyana ko yaushe ne ya afku ba.

A kowace shekara dai, dubban 'yan yankin kahon Afirka ne suke ratsawa mashigin ruwan Yemen da nufin zuwa ci-rani a kasashen Larabawa. Kungiyar Amnesty International ta yi kiyasin cewar a wannan shekara ta 2014 kadai, sama da bakin haure 2500 ne suka nitse a kogi. Sannan kuma wasu karin dubu 150 na kokarin ratsa kogin na Yemen don zuwa wata kasa da ake samun aikin yi cikin sauki.