′Yan gudun hijira na zaman kunci a Libiya | Siyasa | DW | 16.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan gudun hijira na zaman kunci a Libiya

Kungiyoyin fararan hula sun yi wani zama a Nijar domin duba halin kuncin da 'yan gudun hijira 'yan Afirka ke fuskanta a Libiya

Mittelmeer-Flüchtlinge auf der Sea Watch 3 (Sea-Watch/Chris Grodotzki)

'Yan gudun hijirar kashen Afirka cikin kunci a Libiya


A Jamhuriyar Nijar Kungiyar fararan hulla ta Altarenative ce tare da hadin gwiwar hukumar kare hakin bil-Adama ta kasar ta Nijar CNDH, da kuma hukumar kula da ‘yan gutun hijira ta majalisar Dikin Duniya OIM suka yi wani zama domin duba halin kuncin da ‘yan gudun hijira ‘yan Afirka ke ciki a kasar Libiya. An yi mahawara kan wannan batu a bainar jama’a tare da halartar wakillin ofishin jakadancin kasar ta Libiya a Nijar. Lamarin dai ya dauko tushe ne tun bayan da majalisar ‘yan Nijar da ke zaune a kasar Libiya ta hanyar mai kula da hulda da jama’a na majalisar suka zo nan gida Nijar domin sanar da magabata da duk wasu da za su iya taimaka musu kan halin da suke ciki a kasar ta Libiya inda suke zaman ci rani, inda suka ce duk halin da suke ciki na kunci ofishin jakadancin Nijar din a Libiya bai nuna damuwa ba, abin ma da ya sa a wannan mahawara aka gayyaci ofishin ministan harkokin waje na jamhuriyar Nijar kenan domin bada ba’asi kan wannan matsala amma ba tare da sun samu halarta ba. Shugaban hukumar kare hakin bil-Adama ta Nijar ne ya jagoranci buda wannan mahawara kan bakin haure ‘yan Afirka da ke zaune a Libiya.

An dai ga matasa 'yan ci rani da suka fito daga kasashen Liberiya, Najeriya, Senegal, Chadi da kasar Gambiya, wadanda a halin yanzu suke nan birnin Yamai, inda daya bayan daya suka bayyana halin kuncin da suka samu kansu a ciki lokacin suna a kasar Libiya, inda ake sayar da su kamar bayi. A cewar Moutari Gado, wani dalibi a jami’ar birnin Yamai, rashin gudanar da kyakkyawan mulki ne ke sanya ‘yan Afirka yin kwadayin barin kasashensu da zimmar zuwa Turai.
 

Sauti da bidiyo akan labarin