′Yan gudun hijira na Mali a Moritaniya sun yi zanga zanga. | Labarai | DW | 05.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan gudun hijira na Mali a Moritaniya sun yi zanga zanga.

Yan gudun hijirar sun ce suna cikin wani mawuyacin hali na rashin samun kayan abinci saboda jinkiri da hukumomin suke yi ,wajan raraba masu kayan abinci.

Gomai na yan gudun hijirar' na Mali da ke a Moritaniya, sun gudanar da yamutsi a cikin sansanin yan gudun hijira na Mberré da ke a yankin kudu maso gabashi Moritaniya kan iyaka da Malin.Masu aiko da rahotanin sun ce yan gudun hijirar, sun cire shingaye da aka dasa na wayoyi a wurraran da aka girke kayan abincin da a ke raraba masu.

Dangane da yadda suka yi Allah wadai da tsarin raraba abinci wanda sai an ja dogon layi.Wani daga cikin yan gudun hijirar ya ce wata mata ta haifu a cikin layin wajan jiran abinci yayin da wata matar ta mutu.MDD ta ce a kwai yan gudun hijira kusan dubu 18 waɗanda suka samu mafuka a cikin ƙasashe maƙofta na yammanci Afirka; galibi a Moritaniya da Burkina faso tun lokacin da sojojin Faransa suka kutsa kai a yankin arewacin Malin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu