′Yan gudun hijira na kwarara zuwa kasar Kwango | Labarai | DW | 06.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan gudun hijira na kwarara zuwa kasar Kwango

Fiye da mutane 2000 ne ‘yan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka ketara kasar Kwango bayan da suka guje wa tashe-tashen hankulla na baya-bayan nan da ya wakana.

Hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya HCR, tare da hukumar abinci ta duniya PAM ne suka tabbatar da wannan labari, inda suka ce hakan ta faru ne a tsakanin mako daya bayan da rikicin ya tashi. 'Yan gudun hijirar sun isa a yankin Equado da ke Arewa maso Gabashin kasar ta Kwango duk kuwa da cewa a ranar 28 ga watan Satumba da ya gabata ne hukumomin na Kinshasa suka sanar da rufe wannan yanki mai makwabtaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya har ya zuwa wani lokaci a wani mataki na neman kare al’ummarsu da rikicin da makwabciyar kasar tasu ke fama das hi.