′Yan gudun hijira na fuskantar ƙalubale wajen shiga Turai | Siyasa | DW | 23.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan gudun hijira na fuskantar ƙalubale wajen shiga Turai

Miliyoyin mutane na gudun hijira daga Siriya, kuma yawancinsu na ƙoƙarin samun mafaka a Turai to sai dai shugabannin Turan na neman toshe 'yar kafar da su ka samu

Syrian refugees go about their daily lives during a visit by Babatunde Osotimehin (not pictured), Executive Director of the United Nations Population Fund (UNFPA), at the Zaatari refugee camp in the Jordanian city of Mafraq, near the border with Syria April 15, 2013. Osotimehin visited the Zaatari refugee camp in Jordan on Monday to underscore the urgent needs of women and youths affected by the conflict in Syria. REUTERS/Muhammad Hamed (JORDAN - Tags: CIVIL UNREST POLITICS SOCIETY CONFLICT)

'Yan gudun hijiran SIriya a Jordan

Masu neman mafakar siyasa sakamakon rigingimu da kasashensu ke fuskanta, na cigaba da cin karo da matsalolin samun 'yancin shigowa kasashen turai domin samun karbuwa, a kokarinsu na samun ingantacciyar rayuwa.

Fitattun 'yan siyasar nan Jamus kamar Roprecht Polenz na ci gaba da bayyana mamakin yadda 'yan gudun hijirar dake neman inganta rayuwarsu, ke cigaba da fuskantar matsaloli. Yayi tsokaci dangane bukatun da wasu iyalan Siriya ke muradi na karban 'yan uwansu wadanda ke neman mafaka anan Jamus sakamakon yakin basasar da kasarsu ke fuskanta. A tunaninsa dai wannan ba wani abu ne mai wahala ba. Amma sabanin hakan ya gano cewar hakan wani gagarumin aiki ne.

Wer hat das Bild gemacht?: Bettina Kaps Wann wurde das Bild gemacht?: Februar 2009 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Calais, Frankreich Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Bild Nr 7: Von ihrem Lager aus sehen die Flüchtlinge die Fähren nach England – für sie sind sie unerreichbar.

"acewarsu Iyalan nasu sun cimma tserewa zuwa Jordan sa'annan Turkiyya. Shekarunsu 20 anan Jamus, kuma suna da babban gida da zasu iya zama tare da dasu cikin walwala., shin zasu iya zuwa nan Jamuis? Da aka tinkara ni da wannan tambaya da farko dai , na yi tunanin cewar wannan ba wata matsala bace. Amma bayan wasu 'yan bincike da na gudanar na gano cewar, a aikace wannan ba abu ne mai yiwuwa ba".

Matsayin majalisar Turai kan karɓar 'yan gudun hijira

A cewar Dan majalisar tarayya, kuma shugaban komitin kula da harkokin ketare a majalisa Polenz dai, akwai 'yan siriya sama da dubu 40 dake zaune anan Jamus, wadanda asalinsu sun fito ne daga yankunan dake fada da rikici, kuma ke muradin ganin sun karbi 'yan uwansu da a yanzu ke bukatar tallafin mafaka, sai dai sun gaza samun takardun izini bisa dalilan da suka gabatar. Günter Burkhardt dake shugabantar wata kungiyar fafutuka wa 'yan gudun hijira, yayi suka dangane da yadda ake yiwa masu neman mafaka daga wadannan yake yake...

" Kungiyarmu ta yiwa 'yan gudun fafutuka na sane da batutuwan mutane da yawa wadanda keda 'yan uwansu a nan Jamus, amma suna makale a Bulgaria, basu da ikon shigowa nan kasar. Duk da cewar a shirye 'yan uwan nasu suke su karbesu, su basu mafaka, kana suna da sukunin basu kulawar da suke bukata, da ma yiwuwar cudanya. Muna sukar tsarin bada 'yan gudun hijira na tarayyar turai, musamman ma a bangaren kasashen dake watsi da takardun 'yan gudun hijirar idan sun gabatar. Don me 'yan siriya dake neman mafaka zasu makale a Bulgari, idan har 'yan uwasu dama iyalansu baki daya na zaune a arewacin Jamus?".

Jamus ta buɗe ƙofofinta ga masu gudun hijiran Siriya

Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) verfolgt am 18.04.2013 im Deutschen Bundestag in Berlin die Debatte. Im Plenum steht ein Gesetzentwurf des Bundesrats zur Abstimmung, der in Aufsichtsräten börsennotierter Unternehmen die stufenweise Einführung einer Quote für Frauen von 40 Prozent ab 2023 vorsieht. Foto: Wolfgang Kumm/dpa +++(c) dpa - Bildfunk+++ ***FREI FÜR SOCIAL MEDIA***

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

A 'yan makonni da suka gabata dai gwamnatin tarayyar Jamus ta sanar da cewar, a shirye take ta karbi 'yan gudun hijirar kasar Siriya. A rukunin farko dai zata karbi maza da mata kimanin dubu biyar. Kawo yanzu dai babu wata kasa dake cikin tarayyr turai data nuna muradi ko kuma ta taimaka wa 'yan gudun hijira siriya. Mahawarar da ake ji kullum shine, karin kayayyakin agaji a cikin kasar.

Tun shekaru 20 da suka gabata nedai taron kasa da kasa kan kare hakkin bil 'adama a birnin Vienna, ya cimma yarjejeniyar bukatar hadin kan kasashen duniya wajen taimaka wa 'yan gudun hijira. Yarjejeniyar da ta bukaci aiki tare domin cimma wannan manufa, na cire rukunin wasu mutane daga halin kakanuikayi na rayuwa sakamakon halin da suka tsinci kaansu a ciki a kasashensu na asali. Kasashen tarayyar turai dai suna aiki ne da wani tsari na hadin gwiwa na bai daya, dangane yadda suke tinkarar batun 'yan gudun hijira, yarjejeniyar da yanzu haka wa'adinta ya kusan ciki, tsarin da kuma ke ci gaba da samun suka daga masu fafutukar kare hakkin bil'adama.

Mawallafa: Zainab Mohammed Abubakar/Fraczek Jennifer
Edita: Pinaɗo Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin