Yan Gabon sun yi wa Ping lale a Faransa. | Labarai | DW | 29.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan Gabon sun yi wa Ping lale a Faransa.

'Yan kasar Gabon da ke zaune a birnin Paris na kasar Faransa, sun shirya babbar tarba ga madugun 'yan adawan kasar ta Gabon Jean Ping da ke wata ziyara a Faransa.

Madugun 'yan adawar kasar Gabon Jean Ping ya samu gagarumar tarba daga 'yan kasar mazauna birnin Paris na kasar Faransa, inda ya yi kira su tashi tsaye domin ganin sun kwato nasarar da suka samu a zaben da ya gabata.

Cikin jawabin da ya yi a gaban dubban yan kasar da suka zo tarbe shi, Jean Ping ya ce a ranar 27 ga watan Agustan da ya gabata, lalle ne 'yan kasar Gabon sun zabe shi a matsyin shugaban kasa, sai dai gwamnatin kama karya da ke mulki a kasar ta sace wannan nasara tasu a cewar shi.

Babban dan adawan na Gabon ya kuma har yanzu kokawa ba ta kare ba, inda ya ke ci gaba da kin amincewa da kayen da ya sha a wannan zabe wanda ya bai wa Shugaba mai ci Ali Bongo Odimba damar yin tazarce a wani sabon wa'adin mulki na biyu.