1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Faransa na tir da sake fasalin fansho

Mouhamadou Awal Balarabe
January 19, 2023

Dubban dubatan mutane sun fito kan titunan kasar Faransa domin nuna adawa da shirin garambawul ga tsarin fansho da gwamnati ke niyar gudanarwa, lamarin da ya gurganta harkokin sufuri.

https://p.dw.com/p/4MQOL
Masu adawa da tsarin fansho a FaransaHoto: Eric Gaillard/REUTERS

Harkokin sufuri sun gurgance a Paris babban birnin kasar, yayin da matatun man suka tsaya cak, su ma makarantu suka kasance a rufe sakamakon gangamin adawa da tsarin fansho. Dama dai kungiyoyin kwadago da dama sun yi kira ga ma'aikata da su shiga yajin aiki tare da halatar gangamin adawa da wannan mataki. A fiye da garuruwa 200 na Faransa ne wannan gangamin ke gudana .

Ita dai gwamnati na son a kara shekarun yin ritaya daga shekaru 62 zuwa 64. Bugu da kari kuma, adadin shekarun zubin kudin adashin gata don samun cikakken fansho zai karu sannu a hankali. Wannan dai na zama babban kalubale a fannin siyasa ga Shugaba Emmanuel Macron a yanayi na matsin tattalin arziki, duk da danganta shi da yake yi da mataki mai muhimmanci a wa'adin mulkinsa na biyu.