′Yan fafitiki na maraba da matakan ba-sani da Buhari ya dauka | Siyasa | DW | 20.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan fafitiki na maraba da matakan ba-sani da Buhari ya dauka

A Najeriya kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa da ‘yan siyasa sun yi tsokaci kan dakatar da manyan jami’an gwamnati da shugaban kasar ya yi bisa zargi na cin hanci da rashawa bayan dadewa ana korafi a kan lamarin.

Wannan mataki da shugaban Najeriya ya dauka a kan sakataren gwamnati David Lawal Babachir da kuma daraktan hukumar tattara bayanan sirri Ambasada Oke, da ya biyo bayan cece-kucen da aka yi a kan zarginsu da aikata ba dai dai ba a gwamnatin da jagoranta shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin ba sani ba sabo, ko shakka babu ya kama hanyar sauya yadda ake kallon al’amuran cin hanci a kasar. Domin kuwa jinkiri ko rashin daukan mataki a kan wadanda ake ganin sun nuna halin bera ta kai ga na mutanen da ake ganin suna da ikon fada aji, fitowa fili su rubuta wa shugaban wasika, baya ga  fada a baka da ma shagube na cewa basu fa gamsu ba. Wannan ya sanya masu fafutukar kare hakkin jama’a bayyana yadda suke kallon lamarin. Mallam Dantata Mahmoud, shi ne kakakin kungiyar yaki da cin hanci da rashawa da bunksa ci gaba. Ya bayyana cewa dama sun dade suna jiran ganin an dau irin wannan matakin.

Daukan mataki a kan na kusa da shugaba Buhari da ke tabbatar da furucin da ya yi cewar shi fa baya da kowa kuma bana kowa ba ne a tsarin gwamnatinsa, muhimmi ne a yadda ake tafiyar da lamura a kasar. Ko wane tasiri wannan zai yi ga yaki da cin hanci da rashawa a Najeriyar? Barrister Mainasara Umar, mai fafutukatr yaki da cin hanci da rashawa ne a kasar. Yanan mai cewa wannan alamar Buhari ya fara farga da barcin da yake yi.

A baya dai ‘yan adawa sun yi ta koken cewa akwai wadanda suka zama ‘yan lele da aka kasa taba su, duk da zargin da ake yi musu na handamar dukiyar jama'a. Domin kama daga sakataren gwamnatin Tarayya da ake zargin cin hanci a bada kwangiloli, ya zuwa tsabar kudi Naira bilyan 13 da aka gano a wani gida, wanda babban daraktan hukumar tattara bayanan siri ya nuna masaniya da mallakarsu ga hukuma, batu ne da ya girgiza alummar kasar.  Abin jira a ganin  shi ne sakamako na bincike da aka fara a kan wannan badakala da al'umma za ta sa-ido, don ganin mataki na hukunci da za’a dauka ga duk wanda aka samu da laifi.

Sauti da bidiyo akan labarin