1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan ci-rani 46 sun mutu a kokarin shiga Amirka

June 28, 2022

'Yan sanda sun ce yekuwar taimakon da mutanen da ke cikin motar suka yi ce ta janyo hankalin hukumomi zuwa ga motar da ke makare da 'yan ci-rani amma kuma babu iskar shaka.

https://p.dw.com/p/4DLEv
USA | Texas | Menschen wurden in San Antonio tot in einem Lastwagen gefunden
Hoto: Kaylee Greenlee Beal/REUTERS

A Amirka 'yan ci-rani 46 ne kawo yanzu aka tabbatar sun mutu a cikin wata babbar motar  da ke kokarin shigo da su birnin San Antonio na jihar Texas ta barauniyar hanya daga iyakar kasar Mexiko.


Duk da cewa an saba samun irin wannan mutuwa amma lamarin da ya faru a kudu maso yammacin Amirka na cikin munanan haddura da ke sanadiyyar mutuwar 'yan ci-ranin da ke shigowa kasar ta iyakar Mexiko.