′Yan Chadi na gujewa rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 28.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan Chadi na gujewa rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

'Yan kasar Chadi masu dimbin yawa ne ke barin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya inda suke komawa kasarsu ta gado, bayan da rikici ke dada rincabewa.

'Yan Chadi na barin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ne dan gudun fuskantar bita da kulli daga mayakan sa kai Kiristoci ko kuma gungun masu bore da ke zarginsu da hada baki da tsofaffin yan tawayen kasar wanda mafi yawansu Musulmi ne na kungiyar Seleka da suka kori Shugaban kasar Francoir Bozize daga karagar mulki a watan Maris na wannan shekara.

Tuni dai gwamnatin kasar ta Chadi ta dauki matakin kwaso 'yan kasarta daga Jamhuriyar Afirka ta tsakiyar, inda kawo yanzu aka kwaso mutane kusan dubu uku ta jirgin sama kamar yadda hukumar kula da yan gudin hijira ta duniya ta tarayyar Turai ta tabbatar a wannan Asabar din (28. 12. 13).

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Saleh Umar Saleh