′Yan Burkina Faso na tunawa da Thomas Sankara | Siyasa | DW | 14.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan Burkina Faso na tunawa da Thomas Sankara

Magoya bayan tsohon Shugaban Burkina Faso Marigayi Thomas Sankara, sun fara daga muryoyinsu bayan korar da aka yi wa Shugaba Blaise Compaore daga mulkin kasar.

A Wagadugu babban birnin kasar Burkina Faso, 'yan mintoci kadan kafin shiga makarantar gaba da sakandire mai suna Marien N'Gouabi, an yi wani mutum-mutumi na wani littafi da ke bude, saboda a wannan dandali ne ranar biyu ga watan Oktoba na 1983, Thomas Sankara ya yi jawabinsa na siyasa ga al'ummar kasar wanda ake gani a matsayin jawabin juyin-juya halin da ya kawo babban ci-gaba ga kasar ta Burkina Faso. Sai dai duk da cewa yawancin daliban wannan makaranta sun san sunan na Thomas Sankara, amma kuma basu da masaniya kan manyan ayyukan c-igaba da ya yi irin su inganta layin dogo, madatsun ruwa, gidajen ma'aikata da dai sauran ayyuka:

Norbert Tiéndrébeogo na cikin magoya bayan Thomas Sankara kuma ya yi takarar shugabancin kasar a 2005 karkashin wata Jam'iyya mai suna Front des Forces Sankaristes, wanda ya nuna damuwarsa kan yadda da karfi da yaji ake son shafe duk wani kokari da Thomas Sankara ya yi wa kasar. Masu goyon bayan Thomas Sankara da ake kira «Les Sankaristes » sun taka muhimmiyar rawa wajen kifar da gwamnatin Blaise Compaore inji Norbert Tiendrébeogo, inda ya ce zanga-zangar da aka yi a ranakun 30 da 31 ga watan Oktoba da ta rikide ta koma juyin juya hali har ta kawar da gwamnati, sun dade su na tsara ta ta hanyar wayar da kawunan al'umma a kan fidda tsoro.

Thomas Sankara

Kalaman kin jinin gwamnatin da aka yi ta rerawa yayin zanga-zangar a dandalin 'yan kasa, inda aka fara haduwa a ranar 30 ga watan Oktoba, sannan da sharar da aka yi bayan kone-konen da suka bata garin Wagadugu, na nuni da irin halayan 'yan Burkina Faso na tuni da dabi'un Thomas Sankara da ya kawo canji a kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin