′Yan Boko Haram sun mamayi Gombe | Labarai | DW | 14.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan Boko Haram sun mamayi Gombe

Rahotannin da ke zuwa mana daga Najeriya na cewar 'yan Boko Haram sun mamaye garin Gombe da ke a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

Rahotannin dai sun tabbatar da cewar 'yan Ƙungiyar ta Boko Haram ba su gamu da wata turjiya ba wajen mamaye garin,tare kuma da yin kira ga jama'a garin da su ƙaurace wa zaɓuɓɓukan kasar da ke tafe a Najeriyar.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da birnin na Gombe ya fuskanci irin wannan hare-hare daga Ƙungiyar ta Boko Haram ba . Kawo yanzu dai wakilin DW a Gombe ya bayyana cewar jiragen saman yaƙi na gwamnati na ta yin shawagi a sararrin samaniyar birnin, yayin da jama'a kuma ke ficewa daga garin na Gombe dan tsira da rai.

Mawallafi : Yusuf Bala
Edita : Abdourahamane Hassane