′Yan bindiga sun yi garkuwa da minista a Iraki | Labarai | DW | 08.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun yi garkuwa da minista a Iraki

Mai-rikon mukamin mataimakin ministan shari'a ne aka yi garkuwa da shi a yankin arewacin birnin Bagadaza na kasar Iraki.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da mai-rikon mukamin mataimakin minista shari'a na kasar Iraki. Jami'an tsaro suka ce an yi garkuwa Abdel Karim Faris a yankin Arewa maso Gabashin birnin Bagadaza, kuma ya zama garkuwa na biyu cikin mako guda.

Mai-magana da yawun ma'aikatar shari'ar ya ce an yi garkuwa da mataimakin ministan Karim Faris tare da masu kare lafiyarsa biyu. Haka yana zuwa kwanaki hudu bayan garkuwa da 'yan Turkiya 18 masu aiki da kamfanin gine-gine a birnin na Bagadaza. Kasar ta Iraki ta dade ta na fuskantar matsalolin tsaro da tashe-tashen hankula.