1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun sace mutane a Najeriya

November 22, 2022

Sama da mutane 100 ne hukumomi a Najeriya suka tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga dadi suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/4JtKT
Nigeria Abuja | Sicherheitspersonal | Entführte Studenten
Hoto: Nasu Bori/AFP/Getty Images

Rahotanni daga Najeriya sun ce wasu dauke da bindigogi sun shiga kauyuka hudu na jihar Zamfara, inda suka kwashi mutanen da suka hada da mata da kuma kananan yara.

Fiye da mutum 40 aka kwashe daga kauyen Kanwa na yankin karamar hukumar Zurmi, yayin da wasu 37 din su ma aka kwashe su daga kauyen Kwabre, a cewar kwamishinan watsa labara a jihar ta Zamfara, Malam Ibrahim Dosara.

Haka ma a cewar Malam Dosara, an kwashi wasu mutane akalla 38 a kauyukan 'Yankaba da Gidan-Goga cikin kamarar hukumar Maradun.

Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a arewacin Najeriya dai, ta zama wata gagarumar matsalar da ke faruwa ba dare da rana, kama daga cikin gonaki zuwa kan hanyoyi na manyan da kananan garuruwa.