′Yan bindiga sun mamaye Damaturu na Yobe | Labarai | DW | 01.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun mamaye Damaturu na Yobe

'Yan bindiga da ake zaton ‘yan Kungiyar Boko Haram ne sun afkawa garin Damaturu, inda ake jin karar fashewar bindigogi da kuma abubuwa dake kama da bama-bamai.

Mazauna birnin sun bayyana cewa sun wayi garin safiyar Litinin din nan da jin karajin harbin bindigogi da na bama-bamai, lamarin da ya haifar da rudani a daukacin birnin. Bayanai na nuni da cewa ana ci gaba da fafatawa tsakanin ‘yan kungiyar da jami'an tsaro a gurare daban-daban na birnin.

Babu dai cikakken bayanai da guraren da ‘yan bindigar suka kai wannan hari. Amma wani mazaunin garin ya shaidawa wakilinmu na Gombe Al-Amin Suleiman Muhammad ta wayar tarho cewa an ga maharan sun nufi cibiyoyin tsaro da kuma ma'aikatun gwamnati. Kawo yanzu dai hukumomi ba su ce komai ba kan wannan lamarin.

Harin dai na zuwa ne bayan tsawon lokaci da aka samu ana morar zaman lafiya a birnin na Damaturu. Tuni dai shugabannin al'umma da kungiyoyin addinai suka fara yin kira ga al'ummar Najeriya musamman ma na arewacin da su tashi su kare kansu da kansu daga hare-haren ta'addanci da ke faruwa a kasar.

Mawallafi: Al-Amin Suleiman Muhammad
Edita: Mohamadou Awal Balarabe/LMJ