′Yan bindiga sun kashe sojojin Mali 10 | Labarai | DW | 03.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun kashe sojojin Mali 10

Ƙungiyar Ansar-Dine ce ta kai harin a barikin sojan garin Gourma-Rharous mai nisan kilomita 140 da birnin Timbuktu na arewacin ƙasar

Sojojin Mali 10 sun hallaka a cikin wani harin ta'addanci da wasu 'yan bindiga suka ƙaddamar tun da sanhin safiyar Litinin ɗin nan a barikin sojojin garin Gourma-Rharous mai nisan kilomita 140 da birnin Timbuktu da ke a arwacin ƙasar . Wata majiyar sojin kasar ta Mali ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an kai harin ne da misalin ƙarfe 5 da rabi agogon JMT kuma maharan 'ya'yan wata ƙungiyar masu fafutka ce da ke da alaka da kungiyar Ansar-Dine.

Hukumomin soji ƙasar ta Mali sun ce yanzu haka suna ci gaba da gudanar da bincike domin bayar da cikakken rahoto dangane da abun da ya faru.Wannan hari ya wakana ne kwanaki biyu bayan wani harin kwantar ɓauna da wasu 'yan bindigar suka kai wa sojojin ƙasar ta Mali a Nampala da ke a tsakiyyar ƙasar, da shi ma ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin gwamnatin ƙasar Mali guda biyu.