′Yan bindiga sun kashe rayuka a Sokoto | Labarai | DW | 28.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun kashe rayuka a Sokoto

Wasu 'yan bindiga cikin jerin gwanon babura dauke da makamai a Najeriya, sun kashe wasu gwamman mutane a wasu kauyuka biyar na jihar Sokoto da ke arewacin kasar.

Rahotanni dai sun ce mutanen da aka tabbatar barayi ne, sun yi awon gaba da shanu gami da wasu kayayyaki masu daraja, kamar yadda wani mazaunin Masawa, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Jamus, DPA.

Shaidu sun ce 'yan bindigar da yawansu ya kai akalla mutum 100, sun afka wa kauyuka ne da suka hada da Masawa da Dan Aduwa da Kuzari da Garki da kuma Katuma cikin daren da ya gabata, inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi.

Akalla dai maharan sun kashe sama da mutum 70 a lamarin, wanda gwamnan jihar ta Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana kaduwa da faruwarsa.

A 'yan kwanakin nan ne dai gwamnatin Najeriyar, ta aike da jami'an sintiri na musamman don yaki da bata-garin da suka kwashe lokaci suna sheke a aya yankin arewa maso yammacin kasar.