′Yan bindiga sun bude wa wani otel wuta a Cote d′Ivoire | Labarai | DW | 13.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun bude wa wani otel wuta a Cote d'Ivoire

Wasu 'yan bindiga dauke da manyan makamai sun budewa wani otel wuta da ke zama matattarar masu shakatawar 'yan kasashen waje a kasar Cote d'Ivoire.

Wadanda suka gane wa idanuwansu sun shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewar 'yan bindigar wadanda suke sanye da kallaye a fuskokinsu, sun bude wa katafaren otel din shakatawar da ke shake da mutane a cikinsa wuta.

Kawowa yanzu dai hukumomin birnin Abidjan na kasar ba su bayyana ko mutane nawa ne suka mutu da kuma kasashen da suka fito ba.

Hare-hare a kan manyan otel-otel dai na cigaba da zama ruwan dare a kasashen Mali da Burkina Faso, a inda a 'yan kwanankin baya sai da wasu 'yan bindigar suka budewa wasu a kasashen wuta tare da hallaka da dama da ke yawan shakatawa da gidajen otel din.

Tuni hukumomin tsaron Cote d'Ivoire suka dukufa domin gano wadanda suka kai harin.