′Yan Bayelsa na adawar sayar da rijiyoyin mai | Siyasa | DW | 22.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan Bayelsa na adawar sayar da rijiyoyin mai

A'lummar garin Nembe da ke yankin Niger Delta a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da matakin sayar da wasu rijiyoyin mai da kamfanin Shell ya dauka.

Al'ummar garin Nembe da ke jihar Bayelsa a yankin Niger Delta sun gudanar da wata zanga-zangar don nuna rashin amincewa da matakin sayar da rijiyoyin mai da kuma tashoshin tura danyan mai da kamfanin Shell ya dauka, a yunkurin da kamfanin na Shell ke yi na saida wasu daga kadarorinsa na ayyukan hako mai a Najeriya. Al'ummomin dai mazansu da matansu sun ce ba su amince da kin tuntubarsu a wannan harka ba.

Zanga-zangar nuna adawa da sayar da rijiyoyin mai

Öl in Nigeria

Masu zanga-zanga sun kulle wasu Na'urorin kamfanin Shell

DW Hausa ta fara zuwa tashar tura Mai ta 2, wato Nembe 2 Flow station, da kuma ake tura danyan mai daga kimanin rijiyoyi kusan tamanin, kuma a nanne muka iske dandazon al'ummar ta Nembe mazansu da Matansu rike da kwalaye a cikin kananan Jiragen ruwa, inda kuma sukai ta tsallakawa cikin harabar na'urorin ayyukan na mai mallakin kamfanin na Shell suna kuwwa kamar haka.

A wannan zanga-zangar dai, matasan sun kai ga rurrufe tare da kulle duk wata na'urar me aiki ko gunji a wannan tasha ta tura mai ta 2 da ke Nembe din, tare kuma da rataye kyallaye masu nuna alamar ba lafiya, dangane da harkokin aikin mai a wannan yanki,da aka kiyasta na da rijiyoyin danyan mai sama da dari uku.

Al'ummar ta Nembe din dai sunce babban takaicin da ta kaisu ga wannan zanga-zanga , shi ne cewar kamfanin na Shell ya saida kadarorinsa na aikin mai ga wani kamfanin mai na daban,ba kuma da tuntubar al'ummomin ba,da nufin martaba yarjejeniyoyi masu jibi da ci gaban yankin na Nembe da yakamata sabon kamfanin ya yi la'akari da su ba.

Masu zanga-zanga sun like na'urorin kamfanin Shell

Mr Nelson Ebime, shugaban matasa ne a Yankin Nembe din ,kuma yana cikin wannan zanga-zanga.

" Kamar yadda kuke gani,wadannan kadarorin ayyukan hako danyan mai na daya daga ababen tunkaho ga Gwamnatin tarayya,kuma kamfanin Shell da ke aiki anan basa aiki cikin martaba dokoki da duniya ta aminta da su.Shell na aikin hakar mai a shiyyarmu amma bamu da wutar lantarki,ba ruwa,ba asibiti,sannan ga gurbata mana muhalli,tare da kassara duk wata hanya ta rayuwarmu".

Chif Nenge James,basarake ne a shiyyar ta Nembe.

" Sai da kadarori da kamfanin Shell yayi abune na rashin mutunci da ba zamu amince da shi ba,domin tun kishinkishin din da muka ji kan hakan,muka rubuta takardu na korafi,kuma ba'a ji ba,dan haka yau mun rufe wadannan tashoshin tura danyan mai na Nembe".

Yanzu dai wannan zanga-zanga tare da dakatar da ayyukan dukkanin wasu na'urori masu aiki a musamman tashar tura mai ta 2 da ke Nembe din da masu zanga-zangar suka yi,sun ce na wa'adin wata daya ne, kuma bayan wata daya,abin da zai biyo baya ka iya yin muni.

Sauti da bidiyo akan labarin