′Yan awaren Ukraine sun sako jami′an OSCE | Labarai | DW | 03.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan awaren Ukraine sun sako jami'an OSCE

Bayan da suka shafe mako guda suna daure, masu sanya idon Kungiyar tsaro da hadin kan Turai na OSCE ciki har da Jamusawa sun sami damar komawa gida.

Jagoran tawagar masu sanya idon nan ta Kungiyar Tsaro da Hadin Kan Turai wato OSCE wanda 'yan awaren gabashin Ukraine suka sako a wannan sabar, ya bayyana farin cikin sa da wannan cigaban da aka samu, bayan da suka kasance na tsawon mako guda a daure.

Colonel Axel Schneider wanda bajamushe ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Kamfanin dillancin labarun AFP ya rawaito cewa ranar 25 ga watan Afrilu sadda tawagar masu sanya idon ke kan hanyarsu na zuwa Donietsk, inda za su dauki jirgin sama zuwa Berlin domin komawa kasashensu aka cafke su aka kai su yankin Slavyansk. Ko da shi ke, har kawo yanzu, 'yan awaren sun kuma kame wasu manyan birane a yankin gabashin Ukraine, inda suke da karfi sosai.

Sai dai a waje guda kuma kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci da a gudanar da bincike mai zaman kan shi kan mutuwar mutane 42 a yankin Kudancin Ukraine, a tarzomar da ta rutsa da wasu magoya bayan Rasha a wani ginin da ya kama da wuta a Odessa a jiya.

Kantomar da ke kula da harkokin wajen Turai Catherine Ashton ta ce Kungiyar na bakin cikin rahotannin mace-macen da aka samu a Odessa wanda ake kwatantashi a matsayin mafi muni tun bayan da hambararren shugaba Victor Yanukovich ya ficce daga kasar a watan Fabrairu.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe