′Yan aware sun kai sabon samame a Donetsk | Labarai | DW | 02.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan aware sun kai sabon samame a Donetsk

Rahotannin daga gabacin kasar Ukraine na cewa, 'yan awaren gabacin kasar, na kokarin karbe filin jirgin saman birnin Donetsk daga hannun dagarun gwamnati.

'yan awaran gabacin Ukraine masu goyon bayan Rasha, sun kai wani sabon samame a yau din nan filin jirgin saman birnin Donetsk dake a hannun dakarun gwamnatin kasar ta Ukraine, abun dake kara kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita wutar da bengarorin biyu suka rattabawa hannu, yayin da hukumomin kasar Rasha da na Ukraine zasu sake wani zama a birnin Brussel domin tattauna batun samar da gaz.

A halin yanzu dai ana tsinkayar wani babban hayaki tade tashi daga filin jirgin saman, inda kuma ake ci gaba da jin karan manyn bindigogi.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu