′Yan aware na Mali sun kashe mutane uku | Labarai | DW | 18.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan aware na Mali sun kashe mutane uku

Kungiyar Azawad ta arewacin Mali sun kashe sojojin gwamnati 3 a ranar Litanin a garin Bambara Maoude da ke da nisan kilomita dari da garin Tombouctou.

A Kasar Mali mayakan kungiyar 'yan tawaye na kungiyar CMA ta Abzinawa masu rajin samar da kwarya-kwaryar 'yancin gashin kai ga yankin Azawad na arewacin kasar sun kashe sojojin gwamnati 3 a Litanin a garin Bambara Maoude da ke da nisan kilomita dari da garin Tombouctou.

Wani daga cikin shugabannin sojojin kasar Mali da bai so ya bayyana sunansa ba ya kwarmatawa kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP cewa tun da sanyin safiyar Litanin ne mayakan 'yan tawayan Abzinawan suka kaddamar da wanann hari a kansu a daidai lokacin da suke barci.Tuni dai wata tawagar gwamnan jahar garin Tombouctou ta isa a garin na Bambara Maoude domin ganewa idanunta abun da ya wakana.

Ita ma dai rundunar tsaro ta Majalissar Dinkin Duniya a kasar ta Mali wato MUNISMA ta tabbatar da kai wanann hari wanda ta bayyana a matsayin wani keta haddin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma kwanaki uku a kasar wanda dama mayakan kungiyar 'yan tawayen Abzinawan ta CMA ba ta rattaba hannu akai ba.