′Yan al-Shabbab sun sake kwace wasu wurare | Labarai | DW | 03.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan al-Shabbab sun sake kwace wasu wurare

Dakarun Tarayyar Afirka a Somaliya na Amisom sun janye daga wasu mahimman wuraren kasar sakamakon yawaitar hare-haren 'yan kungiyar al-Shabbab.

A cewar hukumomin kasar, janyewar dakarun na Tarayyar Afirka ya shafi yankuna Qoryoley da Awdhegele wadanda suka sake fadawa a hannayen 'yan kungiyar ta al-Shabaab.

A cewar mazauna wannan yanki, tuni dai 'yan kungiyar ta al-Shabbab suka kafa tutarsu a garuruwan da suka kwace, kuma babu sojan kiyaye zaman lafiya ko daya a yankin da ke a nisan km akalla 80 da Mogadiscio babban birnin kasar.

Daga nashi bangare Shugaban gundumar ta Awdegele Mohamed Aweys ya tabbatar cewa shi ma ya fice daga wannan birni.