′Yan Afirka sun taka rawa a gasar Doha | Zamantakewa | DW | 07.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

'Yan Afirka sun taka rawa a gasar Doha

A rana ta karshe ta gasar guje-guje da tsale-tsale na duniya da aka yi a birnin Doha na Qatar 'yan Afirka sun yi nasarar samun lambobin zinare.

Lelisa Desisa dan Kasar Habasha wanda ya lashe gasar gudun yada kanin wani a Doha

Lelisa Desisa dan Kasar Habasha wanda ya lashe gasar gudun yada kanin wani a Doha

'Yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasashen Afirka ta yi musu kyaun rufi a ranar karshe ta gasar duniya da ke gudana a birnin Doha na kasar Qatar, inda akasarinsu wadanda suka zage dantse sun tashi da lambobin zinare. Kwanaki goma aka shafe ana fafatawa a wasanni 49 na maza da na mata kama daga na harbin mashi zuwa ga tsalle-tsalle tsakanin 'yan wasa kimanin 2000 na kasashe 209 na duniya.Za ku iya samun karin bayani a cikin sautin da ke dauke da labarin wasanni a kasa.

Sauti da bidiyo akan labarin