1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Afirka na fuskantar matsala a Turai

March 14, 2017

'Yan Afirika da ke zaune a Turai ba bisa ka'iba ba na cin karo da kalubale wajen samun horo ko aiki saboda rashin takardu. Sannan suna wasan buya da 'yan sanda saboda rashin izinin zaman kasa.

https://p.dw.com/p/2Z8ZT
Brüssel Place Emile Bockstael
Hoto: DW/M. Kübler

 

'Yan Afirika mazauna Turai na fuskantar matsaloli da dama a lokacin da suke kokarin kyautata rayuwarsu. Kafin su shigo nahiyar sun dauka komai na zuwa ne a saukake musamman ma samun kudi. Sai dai Richard Awo mai kimanin shekaru talatin dan asalin Najeriya wanda ke zaune a Jamus sama da shekaru biyar ya ce har yanzu bai cimma burinshi ba.

Ya ce "Mutum ya saki abun da yake yi a gida ya zo Turai don neman kyakkyawar rayuwa, ba abu ne mai sauki ba kamar yadda mutane a Najeriya ke tunawa. Na farko dai mutum sai ya fuskanci matsalar sajewa da jama‘a, sannan ya fuskanci matsalar yare. "

Shi kuwa Joe dan kasar Zimbabuwe  wanda ke zaune a nan Jamus sama da shekaru goma ya nunar da cewar "Mutum zai iya shafe shekaru sama da goma wajen kokarin ganin ya tsaya a kan kafafunsa a Turai. A tawa shawarar idan mutum yana da abin yi a Afirka gwamma ya zauna a can ya fi amfani .”  

Italien Migranten Flüchtlinge Krise Finanzen
'Yan Afirka na yawan shigowa Turai ta kasar ItaliyaHoto: picture alliance/dpa/D.Balducci

Injiniya Ejike Ezejiofor magidanci ne dan asalin Najeriya wanda ke zaune a nan Jamus. Ya bada shawara inda ya ce " Maganar gaskiya zaman wurin nan bashi da sauki ko kadan, amma mutanenmu ba za su gane hakan ba, naso a ce ina da damar bai wa wani ko wata daga cikin masu son zuwa Turai shawara kan mai za su iske in sun iso.

Gazali Soma dan asalin kasar Ghana yayi nashi bayanin kamar haka."Zaman Turai lalai ba kanwar lasa ba ce , yana da matukar wahala sosai. Ko kafin mutum ya sami kanshi lokacin da ya iso, sai ya bata shekaru masu yawa, kafin ya sami aiki.".