1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Afirka na bayyana ra'ayi bisa nasarar Jamus

July 14, 2014

Masu sha'awar kwallon kafa na ci gaba da mayar da martani bisa nasarar da Jamus ta samu na lashe gasar cin kofin kwallon kafa da aka kammala a kasar Brazil

https://p.dw.com/p/1Ccs3
WM 2014 Finale Deutschland Argentinien Jubel
Hoto: picture-alliance/dpa

A kasar Ghana kamar sauran kasashe na Afirka, 'yan kasar sun yi murnar nasarar da Jamus ta yi na cin kofin kwallon kafa da aka kammala a Rio de Janeiro na kasar Brazil inda Jamus ta doke Argentina da ci daya mai ban haushi.

Masoya Jamus a kasar ta Ghana ana iya ganin su a wurare daban-daban musamman wurare na shakatawa da ke manyan biranen kasar, suna ta bayanai game da murna kan nasarar Jamus. Amma akwai wadanda suka nuna goyon baya musamman sanannen dan wasan Argentinan Lionel Messi.

Wannan mutumin mai suna Emmanuel Nettey, ya bayyana dalili kan murnar nasarar kasar ta Jamus:

''Na yi ra'ayin Jamus ne saboda kyawun tsarin wasansu, kuma ba su daga kafa ba sam, har karshen gasar. Saboda haka na yi farin ciki kwarai da gaske''

Wani Kelvin Asante, cewa ya yi:

''Na yi goyi bayan Argentina a wasan na jiya, dalili kuma shi ne saboda son Messi da nake yi.''

Baya ma ga kasar ta Ghana, a kasashen Togo da Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo na cikin miliyoyin wadanda suka yi murnar nasarar Jamus a gasar na bana.

Vorschau Finale WM 2014 Deutschland Argentinien Fans
Hoto: Getty Images

Wannan mutumin, dan kasar Togo ne.

"Ban yi zaton zan ga Argentina su yi wasa kamar yadda suka yi, na yi zaton Jamus za su mamaye komai amma sai abun ya zama wani iri saboda 'yan Argentina sun buga kwallo. Amma duk da haka na san Jamus za ta ci kwallon."

Wannan dan Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango ya bayyana yadda ya ji da nasarar ta Jamus.

"Na ji takaici, saboda mai goyan bayan Barca ne ni, wannan shi ne dalili na goyan bayan Argentina, amma duk da haka ina yiwa Jamus murna saboda sun kai matsayin ayi musu jinjina."

Baya ga wadannan, akwai wasu dumbin masu bin mu ta shafin Facebook da suka bayyana farin ra'ayi bisa nasarar da kasar ta Jamus ta samu.

WM Finale Brasilien 2014 Joachim Gauck und Angela Merkel
Shugaban kasar Jamus Joachim Gauck da Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: picture-alliance/dpa

Mai Bechir Salif Galadima daga Najeriya ya ce; Ina taya Jamus murna. Sun ci kofin mafi kayatarwa a tarihin kwallo. Lallai sun taka rawar gani.

Alh Ibraheem Dangote El-Karaduwa shima ya ce: Ai dama babu kasar da ta cancanci cin kofin duniya kamar Jamus, domin sun fi kowace kasa 'yan wasa. Muna taya su murna

Muhammad Awwal Bagama cewa ya yi: Duk wanda ya kalli wasa jiya yasan babu wani rikici a ciki an fi Argentina a wasan nan kawai, hakika Jamus muna taya ki murna da farin ciki.

Sai shi kuwa Yusuf Ibrahim Jangeru da ya ce: Muna taya Jamus murnar lashe wannan gasar. Dama idan gwamnatinku ta kyau, komai naku zai yi kyau.

Mawallafi: Muntaqa Ahiwa
Edita: Suleiman Babayo