′Yan Afirka da ke da niyar yin kaura | Zamantakewa | DW | 19.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

'Yan Afirka da ke da niyar yin kaura

'Yan Afirka da ke zaune a Equatorial Guinea na daf da yin kaura saboda matsalar tattalin arziki da kasar ke fuskanta

 

Dubban 'yan kasashen Afirka ne da ke zaune a kasar Equatorial Guinea, a maimakon zuwa wasu kasashe kamar su Turai da Amirka,A yanzu suke yin tunanin sauya sheka zuwa wasu kasahe na Turai.Kasar Equatorial Guinea dai na kumshe ne da dubban mutane 'yan asalin yammacin Afirka da suka zo wannan kasa mai arzikin man fetur da kuma a baya take da karfin tattalin arziki. Sai dai faduwar darajar kudaden danyan mai a kasuwanni duniya, ya saka wannan karamar kasa mai arzikin man fetur  cikin mawuyacin hali na tattalin arziki, inda 'yan ciranin na yammacin Afirka ke fuskantar babban kalubale na rayuwa. Kamar yadda wani da ya fito daga kasar Togo mai suna Bello Rafiou ke tsokaci:" A halin yanzu dai lamarin ya yi kamari, idan kana bukatar abinci, kai ko fita ma matsala ce lamarin ya yi tauri."

Wasu dai na kiran wannan kasa ta Equatorial Guinea Koweit ta Afirka, yayin da wasu ke kiranta wurin jin dadi, kuma baya ma ga 'yan kasashen Afirka ta yamma, akwai kuma dubban jama'a 'yan asalin kasashen tsakiyar Afirka kamar irin su Kamaru da Chadi, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Sai dai a halin yanzu dukkanninsu gwiwoyinsu sun yi sanyi da wannan kasa, ganin cewar sun zo ne domin samun arziki su koma kasashen su, wanda yanzu masu sha'awar bin hanya ta ruwa domin zuwa Turai na dada karuwa.