1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Turkiyya zai fuskanci kalubalen zabe

Suleiman Babayo AS
March 7, 2023

Gamayyan 'yan adawa na Turkiyya sun amince da Kemal Kilicdaroglu a matsayin dan takara guda na bangaren adawa a zaben shugaban kasa domin fafatawa da Shugaba Recep Tayyip Erdogan a zaben shugaban kasar da ke tafe.

https://p.dw.com/p/4OMpl
Turkiyya, Ankara | Gamayyan 'yan adawa sun amince da  Kemal Kılıçdaroğlu dan takara guda na shugaban kasa
Kemal Kılıçdaroğlu dan takara na 'yan adawan TurkiyyaHoto: Evrim Aydin/AA/picture alliance

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya yana fuskantar kalubale mafi girma tun lokacin da ya dare madafun iko kimanin shekaru 20 da suka gabata, yayin zaben watan Mayu da ke tafe. Kasar tana cikin matsanancin tattalin arziki sakmakon yakin Ukraine da rikice-rikice a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

Shugaba Erdogan yana takara yayin zaben ranar 14 ga watan Mayu mai zuwa inda za a fafata a zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki, watan bayan girgizar kasa ta halaka dubban mutane.

A bangaren 'yan adawa sun dunkule waje guda inda Kemal Kilicdaroglu yake takara karkashin gamayyan 'yan adawa, wadanda suke neman kawo karshen manufofin da suka jefa kasar ta Turkiyya cikin matsalolin da take fuskanta.