'Yan adawan Siriya sun sauya alƙiblarsu
September 22, 2013'Yan adawan Siriya sun yi amai sun lashe bayan da suka dawo suka ce zasu kasance a tattaunawar sulhun da kasashen Rasha da Amirka za su gudanar a ƙasar Switzerland, wanda daga farko suka ce sun janye. Manufar duk waɗanda za su kasance a wannan taron dai shine girka gwamnatin riƙon ƙwarya mai cikakken iko, a cewar shugaban majalisar 'yan adawan Siriyar Ahmad al-Chader, cikin wata wasiƙa da ya rubutawa Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya.
Su dai 'yan tawayen na Siriya sun haƙiƙance kan cewa shugaban ƙasa Bashar al-Assad, ko ɗaya ba shi da wata rawar da zai taka a gwamnatin riƙon ƙwaryar da za a girka.
A na sa ɓangaren shugaba Bashar al Assad ba shi da niyyar barin madafun ikon ƙasar. Gwamnatin Jamus a nata waje kuma tana shirin ƙaddamar da wani sabon shirin diplomasiyya domin shawo kan wannan matsala na Siriya.
A cewar ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, yanzu kowane ɓangare na sane da cewa matakin soji ba zai yi nasara wajen dakatar da yaƙin basasar ba. Kuma a dalilin haka ne a mako mai zuwa lokacin taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, Jamus za ta matsa ƙaimi wajen ganin an tsagaita wuta a Siriya.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal