′Yan adawan Nijar na kalubalantar gwamnati | Siyasa | DW | 27.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan adawan Nijar na kalubalantar gwamnati

kawancen Jam'iyyun siyasa na ARDR a Jamhuriyar Nijar sun gudanar da gangami a Damagaram bayan da zanga-zangar lumana da suka shirya ta kasa samun karbuwa.

'Yan adawan Nijar na ARDR sun yi niyar tayar da magoya bayansu daga barci ta hanyar shirya zanga-zangar lumana dangane da wainar siyasar da ake toyawa a kasar. Sai dai kuma hakarsu ta birnin Damagaram ba ta cimma ruwa ba. Saboda haka ne suka gudanar da gangamin a Zinder din.

Gwamnan Jahar Damagaram ya ce ya haramta zanga zangar ne saboda wakilan 'yan adawa ba su cika sharuda ba. Sannan ya ce duk yunkurin da ya yi na yin magana da su ta waya ya yi tura.

Magoya bayan sun ta rera kalaman rashin son salon mulki da suka kira na "danniya da buri " da gwamnatin Mahamadou Issoufou ke gudanarwa. Dalili kuwa shi ne, jami'an tsaro sun yiamfani da barkono mai sa hawaye wajensu tarwatsasu, a lokacin da suka yi shiri don gudanar da zanga-zanga lumana. Daga cikin wadanda suka halarci gangamin har da madugun 'yan adawa Seyni Omar da kuma Hama Amadou, shugaban jam'iyyar Moden Lumana Africa, kana kakakin majalisa.

Jagororin adawar dai sun yi kaca-kaca da aikace- aikacen da gwamnatin Jamhuriyar ta bakwai ta yi a tsawon shekarun nan uku, inda suka zargeta da aikata almundahana da rashawa tare da take dokokin kasa.

Mawallafi: Larwana Malam Hami daga Damagaram
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin