1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawan Kwango sun ƙauracewa shirin haɗin kan 'yan ƙasa

September 2, 2013

Yunƙurin gudanar da sauyin da zai samar da ci-gaban ƙasa na yin karo da cikas a ƙasar Kwango, bayan da 'yan adawa suka nuna rashin gamsuwarsu da matakan shugaba Joseph Kabila

https://p.dw.com/p/19aPS
Democratic Republic of Congo President Joseph Kabila attends the signing ceremony of the Peace, Security and Cooperation Framework for the Democratic Republic of Congo and the Great Lakes, at the African Union headquarters in Ethiopia's capital Addis Ababa Feburary 24, 2013. A U.N .-mediated peace deal aimed at ending two decades of conflict in the east of the Democratic Republic of Congo was signed on Sunday by leaders of Africa's Great Lakes region in the Ethiopian capital Addis Ababa. REUTERS/Tiksa Negeri (ETHIOPIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Shugaba Joseph KabilaHoto: Reuters

Jagororin jamiyyun adawa uku a ƙasar Kwango sun ce za su ƙauracewa tattaunawar da aka shirya gudanarwa wannan makon da burin samar da sulhu tsakanin 'yan ƙasa.

Wannan mataki da suka ɗauka ya kawo cikas ga yunƙurin shugaba Joseph Kabila na samar da sulhu da haɗin kan 'yan ƙasa a daidai lokacin da yake cin karo da adawa daga yankin gabashin ƙasar.

Daga cikin waɗanda zasu ƙauracewa tattaunawar har da magoya bayan madugun 'yan adawa Etienne Tshisekedi wanda ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a shekarar 2011.

Sharaɗin da 'yan adawar suka bayar na komowa wannan tattaunawa shi ne samar da mai shiga tsakani wanda baya goyon bayan kowane ɓangare kafin su amince su shiga.

Shugaba Kabila ya yi alƙawarin gudanar da sauye-sauyen da zasu haɗa kan yan ƙasar, wadda ke da faɗin ƙasashen yammacin Turai ɗungun, wadda kuma ta mallaki ɗimbin albarkatun ƙarƙashin ƙasa, to sai dai yawan tashe - tashen hankula na kawo tsaiko wajen gudanar da ayyukan ci-gaban ƙasa.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu