′Yan adawan Ghana sun nufi kotu | Labarai | DW | 11.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawan Ghana sun nufi kotu

Babbar jam'iyyar adawar kasar Ghana ta bayyana cewa za ta kalubalanci sakamakon zaben Shugaban kasa a gaban kotu

Babbar jam'iyyar adawar kasar Ghana ta bayyana wannan Talata cewar za ta kalubalanci sakamakon zaben Shugaban kasa da aka gudanar ranar bakwai ga wannan wata na Disamba a gaban kotu.

Wani babban jami'in jam'iyyar ta tabbatar da shirin kalubalantar zabe wa kamfanin dillacin labaran Reuters.

Jam'iyyar ta NPP wadda Nana Akufo-Addo ya yi mata takara ta ce akwai wurare masu yawa da aka karya dokokin zabe, da gudanar da rashin gaskiya.

Sakamakon zaben da hukumar zabe ta fitar ya nuna Shugaba John dramani Mahama na jam'iyyar NDC mai mulki ya lashe zaben da kashi 50.7 cikin 100 na kuri'an da aka kada, yayin da Nana Akufo-Addo na jam'iyyar adawa ta NPP ya zo na biyu da kashi 47.7 cikin 100.

Kuma daruruwan magoya bayan jam'iyyar adawar sun fito kan titunan Accra babban birnin kasar ta Ghana, a wannan Talato domin nuna rashin gasuwa da sakamakon zaben shugaban kasar. Duk wani tashin hankali zai iya jefa kasar cikin kasada, duk da ya ke tana cikin kasashen Afirka da ake yaba musu wajen gudanar da demokaradiyya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal