1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa za su kaurace wa zabe

Suleiman BabayoJune 11, 2015

Gamayyar jam'iyyun adawa 17 na kasar Burundi sun kudiri aniyar kaurace wa zaben kasar

https://p.dw.com/p/1FfwO
Burundi Proteste gegen Präsident Nkurunziza Demonstration
Hoto: Getty Images/AFP/J. Huxta

Gamayyar jam'iyyu adawa 17 na kasar Burundi sun kudiri aniyar kaurace wa zaben kasar, saboda zargin rashin kwantana adalci. 'Yan adawa sun yi kuma zargin cewa hukumar zaben kasar ba ta da cikakkun mambobi saboda biyu daga cikin mambobin sun tsere sakamakon rikicin siyasa.

Kasar ta Burundi ta fada cikin rudanin siyasa tun lokacin da Shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana shirin sake takara a karo na uku, abin da suke cewa ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.

Kimanin mutane 20 sun hallaka yayin da daruruwa suka samu raunika lokacin fito na fito tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaron. Gwamnatin kasar ta Burundi ta ce an kawo karshen zanga-zangar ta nuna adawa da shirin Shugaba Nkurunziza na nenam tazarce. Za a yi zaben 'yan majalisa ranar 29 ga watan Yuni sannan zaben shugaban kasa ranar 15 ga watan Yuli.