′Yan adawa za su kalubalanci Yahya Jammeh | Labarai | DW | 31.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawa za su kalubalanci Yahya Jammeh

A Gambiya Hadin gwiwar kungiyoyin 'yan adawa sun zabi dan takara daya lak tilo wanda zai kalubalanci shugaba Yahya Jammey a zaben shugaban kasa.

Adama Barrow dan shekaru 51 jagoran jam'iyyar UDP shi ne hadin gwiwar jam'iyyun siyasar na adawa guda bakwai suka wakilta ya tsaya takara a zaben na watan Disamba da ke tafe,wanda shi ne karo na biyar ke'nan da Yahya Jammey zai yi takara.Jammeh wanda ya zo kan karagar mulki bayan wani juyin mulkin a shekara ta 1994  kafin ya rikide ya koma farar hula kungiyoyi  masu fafutuka  da na 'yan adawar kasar da kuma 'yan jaridu na zarginsa da take hakin bil Adama.