′Yan adawa sun lashe zaben tsibirin Cape Verde | Labarai | DW | 21.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawa sun lashe zaben tsibirin Cape Verde

'Yan adawa sun lashe zaben majalisar dokokin tsibirin Cape Verde karo na farko cikin shekaru 15.

'Yan adawa a tsibirin Cape Verde sun lashe zaben majalisar dokoki a zaben da ya gudana wannan Lahadi da ta gabata. Babbar jam'iyyar adawa ta Movement for Democracy ta sake dawowa kan madafun iko bayan adawa na tsawon shekaru 15. Ita kuma jam'iyya mai mulki ta PAICV ta samu kashi 37 cikin 100.

Portugal ta yi wa tsibirin na Cape Verde da ke yammacin Afirka mulkin mallaka kuma yana makwabtaka da kasar Senegal, tsibirin ya kauce wa duk rikice-rikicen siyasa da suka ritsa da yankin na yammacin Afirka a shekarun da suka gabata. Kuma wani lokaci cikin wannan shekara za a gudanar da zaben shugaban kasa na kasar ta Cape Verde.