′Yan adawa sun gurbata zabe a kasar Cote d′Ivoir | Labarai | DW | 30.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawa sun gurbata zabe a kasar Cote d'Ivoir

Ministan cikin gidan kasar Cote d'Ivoir Hamed Bakayoko, ya yaba yadda zaben rabagardama kan sabon kundin tsarin mulkin kasar ya gudana, duk kuwa da tarin matsalolin da ya ce an samu a wasu yankunan kasar.

Zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki da ya gudana a wannan Lahadi a kasar Cote d'Ivoir, ya gamu da tashe-tashen hankulla a wurare da dama, inda gungun matasa suka yi ta kai farmaki a runfunan zabe tare da dagula harkokin zaben, yayin da a wasu wuraran ma suka rin ka kwace akwatunan zabe. 

Wuraran da aka samu tarin matsalolin dai sun hada da unguwannin Yopougon da Marcory da ke da cinkoson jama'a na birnin Abidjan da kuma birnin Gagoa mai nisan km 270 a yammacin birnin na Abidjan, da ke a matsayin yankunan da tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo ke da karfi, irin su Divo da Daloa da kuma birnin Dabou.

Ministan cikin gidan kasar ta Cote d'Ivoir  Hamed Bakayoko ya yi batun wasu runfunan zabe akalla 100 da aka samu matsala, amma kuma ya ce duk da haka harkokin zaben sun cigaba da gudana a kasar. 'Yan adawan kasar dai sun yi kira da a kaurace wa zaben, inda suke zargin hukumomin kasar da yin gaban kansu ba tare da saka 'yan adawa ko kungiyoyin fararan hulla cikin lamarin ba.