′Yan adawa a Nijar sun koka kan kame-kame | Siyasa | DW | 08.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan adawa a Nijar sun koka kan kame-kame

Sabon kawancen Jam’iyyun adawa mai taken “Adawa mai zaman kanta” sun bukaci hukumomin Jamhuriyar Nijar da su gaggauta sako manbobin kawancen 10 da jami’an tsaro suka cafke lokacin gangami.

Tun a karshen mako ne 'yan sanda suka kame mambobin kawancen yayin wani zaman dirshin don nuna adawa da sabon kasafin kudin bana da nuna adawa da kasancewar sojojin kasashen ketare a sansanoni daban daban a Nijar. Sai dai hukumomin kasar na zargin 'yan adawar da tada zaune tsaye ta hanayar shirya zanga-zanga ba tare da izini ba.

Shugabar kawancen 'yan adawar Mme Bayard Hajiya Mariama Gamatche ta shedawa DW cewa "Kamen da 'yan sanda suka wa manbobin su abu ne da baya da hujja." 

A ranar Alhamis ne ya dace a gabatar da mambobin sabon kawancen da aka kama a gaban Alkali, sai dai bayan magoya bayan jam'iyyun daban daban ciki har da na kawancen adawa, sun yi cincirindo a gaban kotu. Wasu rahotanni sun ce an sake tsawaita wa'adin rike wadanda aka kama har izuwa ranar Jama'a.

Kawancen 'yan adawar da ya shirya gangamin na ci gaba da nesanta kansa da aikata laifi, yanzu dai hankali ya karkata kan abinda zai je ya komo ganin cewar wannan shi ne karon farko da aka kama wasu manbobin sabon kawancen.