´Yan adawa a Kenya sun yi iƙirarin yin nasara a zaɓen shugaban ƙasa | Labarai | DW | 29.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan adawa a Kenya sun yi iƙirarin yin nasara a zaɓen shugaban ƙasa

Magoya bayan shugaban ɗan adawa a Kenya Raila Odinga sun yi ikirarin lashe zaben shugaban ƙasar da aka gudana a ranar alhamis. To amma bayan kammala ƙidayar kashi uku cikin hudu na ƙuri´un da aka kada a gundumomi, hukumar zaɓe ta ƙasar ta Kenya ta ce Odinga ke kan gaba da yawan ƙuri´u da ya kai kashi 49 cikin 100 yayin da shugaba mai ci Mwai Kibaki ya ke da kashi 45 cikin 100. Da farko magoya bayan Odinga sun ta da tarzoma don nuna rashin jin dadinsu dangane da jinkirin da ake samu wajen tattara sakamakon zaɓen. Wakilin jam´iyar ´yan adawa ta ODM, William Ruto ya ce dagangan hukumar ke yin haka.