′Yan adawa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun ƙaurace wa shiga sabuwar gwamnati. | Siyasa | DW | 02.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan adawa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun ƙaurace wa shiga sabuwar gwamnati.

Sabuwar majalisar ministoci da shugaban gwamnatin mulkin soji Michel Djotodia ya naɗa, ta yi zaman taronta na farko, sai dai ba tare da halartar wasu gungun ministocin na adawa ba.

Gwamnatin ta haɗin kan ƙasa wace pirayim mistan Nicolas Tiangaye ya naɗa, ta ƙunshi manbobi 34 waɗanda suka haɗa da wakilan tsohuwar ƙungiyar 'yan adawar da na yan' tawaye da kuma na ƙungiyoyin fara hula.

Yan adawar sun ce suna buƙatar samun ƙarin haske akan gwamnatin riƙon ƙwarya

Partisans of new Central African Republic leader Michel Djotodia hold flags and banners during a support march in the streets of Bangui on March 30, 2013. The Central African Republic's new strongman Michel Djotodia vowed Saturday not to contest 2016 polls and hand over power at the end of the three-year transition he declared after his coup a week ago. (banner reads; 5th districj, Banda-GB quarter, Yes to change, Support the President Michel Djotodia Am Nondroko '). AFP PHOTO / SIA KAMBOU (Photo credit should read SIA KAMBOU/AFP/Getty Images)

Al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

A cikin wata sanarwa da suka bayyana haɗin gwiwar jam'iyyun siyasar da suka yi adawa da tshohuwar gwamnatin Francois Bozize, wanda yan tawayen Seleka suka hamɓarrar a cikin watan jiya. Wadanda suka haɗa da MLPC sun sanar da cewar sun dakatar da shiga gwamnatin. Josephe Benduga Tsohon magajin garin Birnin Bangui, na ɗaya daga cikin shika shikan ƙawancen jam'iyyun siyasar. Ya ce : ''Ni kai na, da na ke yin magana da ku minista ne, na kiwo. Ya ce kuma ban halarci wannan zaman taro na majalisar ministocin ba, tare da ni a kwai ministocin da ba su halara ba. Amma ya ce duk da haka a kwai wasu daga cikin mu, waɗanda suka shiga taron, ya ce wannan ya yi ruwan su, ya ce kuma jam'iyyun siyasar da waɗannan maya gurbi suka fito alhaki ya rattaya akan su na ɗaukar nauyin lamarin.''

Taron ƙasashen yankin Tsakiyar Nahiyar Afirka zai tattauna rikicin siyasar ƙasar

Central African Republic peace talk participants, including Seleka rebel alliance leader Michel Djotodia, left, and Jean Willybiro Sako, second left, head of the Central African Republic's government delegation, sign a peace agreement, in Libreville, Gabon, Friday, Jan. 11, 2013. Officials say that the rebel group controlling much of the northern half of the Central African Republic have agreed to enter into a coalition with the government. The deal will allow President Francois Bozize to stay in office until his current term expires in 2016. (AP Photo/Joel Bouopda Tatou)

Taron Tattaunawa tsakanin ' Yan siyasar Afirka ta Tsakiya

Shida daga cikin ministocin guda tara na yan adawa a ciki haɗa pirayim ministan sun jadada kasancewa a cikin gwamnatin haɗin kan ƙasar. Tare da bayyana aniyarsu ta yin aiki domin ci gaban ƙasar da ke fama da matsalar talauci. Duk kuwa da arzikin ma'adinai da Allah ya albarkaci ƙasar da su, Josephe ya bayyana dalilansu na ƙauracewa gwamnati. Ya ce: ''Buƙatar mu ga Tchangaye shi ne cewar ya kamata a fayace mana dala dala tsarin da aka yi na gwamnatin riƙon ƙwaryar domin kada a bar mu cikin duhu, ta yada dukkanin sauran sassan da suka halarci yarjejeniyar Libreville zasu amince da tsarin.''

Yanzu haka dai al'amura sun fara daidaita a ƙasar inda bankuna da shaguna suka sake buɗewa a daidai lokacin da ƙasashen yankin na Tsakiyar Afirka zasu soma wani taro a gobe a birnin Ndjamena wanda zai tattauna rikicin siyasar na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto , sannan kuma a kwai rahoton da Lateefa Mustapha Ja'afar ta haɗa mana akan Jana'izar Sojojin Kasar Afrika ta Kudu 13 da aka kashe a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin