′Yan adawa a Indiya sun soki gwamnati kan Covid-19 | Labarai | DW | 13.05.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawa a Indiya sun soki gwamnati kan Covid-19

Manyan jami'iyyun adawa na Indiya sun bukaci matakin gaggawa domin shawo kan annobar annobar cutar coronavirus da ta ta'azzara a kasar.

Manyan jam'iyyun adawa 12 na kasar Indiya sun bukaci Firamnista Narendra Modi ya dauki matakai cikin gaggawa domin dakile yaduwar annobar cutar coronavirus da kasar ta samu kanta a ciki, inda dubban mutane suka halaka. Rahul Gandhi shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Congress ya zargin firamnistan da kawar da kai kan karancin allurar rigakafin cutar, da rashin iska shaka da magunguna.

A wannan Alhamis fiye da mutane 4,000 cutar ta coronavirus ta halaka kuma kwanaki hudu a jere sabbin kamuwa da cutar sun kusan kai wa 400,000 a kasar ta Indiya ta biyu wajen yawan mutane a duniya.