′Yan adawa a Haiti sun ki amincewa da sakamakon zabe | Labarai | DW | 17.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawa a Haiti sun ki amincewa da sakamakon zabe

Mutane fiye da dubu biyu ne suka yi zanga-zanga a birnin Port-au-Prince na kasar Haiti domin nuna adawarsu da sakamakon zaben shugaban kasar wanda Jovenel Moïse ya lashe da kashi 55.67 cikin 100.

Daya daga cikin 'yan takarar neman shugabancin kasar Haiti Moise Jean Charles, ya kasance cikin masu zanga-zangar inda ya ce masu hannu da shuni na kasar ne ke son tilasta musu wannan shugaba yana mai cewa: "Mutane uku ne daga cikin manyan masu kudin wannan kasa ke son tilasta mana wanda suke so a matsayin shugaban kasa, don haka mun ce hakan ba za ta sabu ba, sun wallafa sakamakon da mu ba mu yarda da shi ba, yanzu kuma yaki ne muke yi na siyasa da kuma na shari'a. Tun da a hannu daya mun shigar da kara a kotu, a dayan hannun kuma mun fito bisa titi."