1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa a Banizuwela sun mamayi kujerun majalisa

Yusuf BalaDecember 7, 2015

Ya zuwa yanzu wannan jam'iyya ta adawa ta samu kujeru 99 a majalisar dokokin kasar mai kujeru 169 a cewar hukumar zaben kasar.

https://p.dw.com/p/1HIPe
Venezuela Wahlen Nicolas Maduro
Shugaba Nicolas MaduroHoto: Reuters/Miraflores Palace

'Yan adawa a kasar Banizuwela sun samu gagarumin rinjaye a zabukan majaliasar dokokin kasar wani abu da ya girgiza jam'iyya mai mulki da ke jan ragamar wannan kasa tsawon shekaru 17 karkashin gurguzu.

Ya zuwa yanzu wannan jam'iyya ta adawa ta samu kujeru 99 a majalisar dokokin kasar mai kujeru 169 a cewar hukumar zaben kasar. Ita kuwa jam'iyya mai mulki ta samu kujeru 46, yayin da ake sa ran aji mokamar sauran kujeru 19 abin da dai ke nuna cewa jam'iyyar adawa ta samu dama ta kalubalantar Shugaba Nicolas Maduro.

Al'ummar wannan kasa dai a birnin Carcas sun fantsama tituna dan nuna murna ga wannan nasara ta 'yan adawa abin da ke nuna cewa sun gaji da salon mulki irin na gurguzu a kasar.