′Yan Ƙungiyar Boko Haram sun ƙwace garin Michika | Labarai | DW | 07.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan Ƙungiyar Boko Haram sun ƙwace garin Michika

Rahotanni daga Jihar Adamawa da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewar 'yan Ƙungiyan Boko Haram sun karɓe iko da ƙaramar hukumar Michika.

Shaidu mazauna garin na Michika sun shida wa DW cewar 'yan ƙungiyar sun kafa tuttarsu suna kuma ta yin sintiri a cikin garin, yayin da jama'ar garin suka kiɗime suna ƙoƙarin ƙaurace wa birnin.

Kuma a halin da ake ciki al'ummar ƙaramar hukumar Mubi na cikin zaman ɗar-ɗar da kuma fargabar abin da ka iya biyo baya inda tuni wasu suka soma ficewa daga yankin.

Mawallafi : Abdulraheem Hasan / Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal