'Yan ƙasar Zimbabwe sun fito don jefa ƙuri'a
July 31, 2013A ƙasar Zimbabwe an buɗe rumfunan zaɓe, don zaɓar sabon shugaban ƙasa da 'yan majalisun dokoki. Daga cikin 'yan takara biyar, waɗanda suka fi fice sune Morgan Tsvangirai ɗan shekaru 61 a duniya na jami'iyyar MDC, sai kuma shugaba Robert Mugabe ɗan shekaru 89 da haifuwa na ZANU-PF, wanda ke mulkin ƙasar tun bayan samun yancin kai a shekara ta 1980. Wani ɗan takarar da zai yi tasiri a zaben na Zimbabwe shine Dumiso Dabengwa. Ya kasance tsohon ministan harkokin cikin gida a gwamnatin Mugabe, amma yanzu shi ne shugaban jam'iyyar ZAPU da ya sake farfaɗowa. Jam'iyyar dai ta sake samun 'yan zaman kanta bayan da ta balle daga haɗakar ta tilas da jam'iyyar Mugabe ta ZANU-PF a shekara ta 1989. A shekara ta 2008 dai Dabengwa ya goyi bayan 'yan adawa, amma a yanzu shi kansa zai ƙalubalanci Mugabe a wannan zaɓen.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Uamru Aliyu