Yamutsin ′yan makaranta a Nijar | Siyasa | DW | 18.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yamutsin 'yan makaranta a Nijar

Ƙungiyar daliban ƙasar ta tabbatar da mutuwar dalibi ɗaya yayin da 'yan sanda suka tsare sama da guda goma a lokacin wata zanga-zanga a birin Yamai.

Dubban ɗaliban ne suka gudanar da zanga-zangar a duk faɗin birnin Yamai inda suka riƙa yin ƙone-ƙone na tayoyi a kan tituna. Jamian 'yan sanda masu kwantar da tarzoma sun yi amfani da kulake domin tarwatsa daliban waɗanda suka yi jerin gwano daga makarantunsu zuwa majalisar dokokin ƙasar domin nuna ɓacin ransu, dangane da matsalar ƙarancin malamai da ake fuskanta da kuma sauran kayayyakin aiki watannin biyu bayan soma karantun.

An jibge jamian tsaro a gaban majalisar dokokin

Gebäude des Parlaments der Republik Niger, Niamey. Foto: Mahaman Kanta/DW, 19.5.2011, Niamey / Niger, Zulieferer: Thomas Mösch

Majalisar dokokin Nijar

Ɗarurruwan 'yan sandar kwantar da tarzoma ne suka ja daga a gaban majalisar domin taka birki ga daliban da suka bazu ko'ina a kan tituna suna yin ƙone-ƙone.Dalibban dai sun taso ne tun da sanyin safiya daga makarantunsu daban-daban domin zuwa majalisar da nufin kai kokensu ga wakilan ƙasar. A kan hanyarsu ta komawa makaranta na haɗu da wasu daliban inda ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar tasu mai suna Sumana Altine Bureima ya yi ƙarin bayyani a kan dalilan yin wanann zanga-zanga. Ya ce : ''Kun san shugaban ƙasa ne ya ɗaukar mana alƙawari da zai gina mana ɗakunnan ɗaukar darasi inda zamu karatu, mun yi yarjejeniya suka ce mana zuwa ranar 15 ga wanann wata na Nuwamba komai zai daidaita amma har yanzu shuru ne.''

Daliban sun haddasa babbar ɓarna a cikin gari

Wer hat das Bild gemacht?: Salissou Boukari Wann wurde das Bild gemacht?: 19.5.2011 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Tahoua / Niger Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Erster Schultag für Oberschüler in Tahoua, Republik Niger.

'Yan makaranta a jihar Tahoua,

A gaban majalisar dokokin daliban sun yi nasarar karkashe kayayyakin lantarki na majalisar tare da ƙona motocin jama'a da dama. Amma kuma ƙungiyar dalibban ta bakin mataimakin magatakardan ƙungiyar daliban na ƙasa wato USN ,ta tabbatar da mutuwar wani ɗalibi guda a yayin da wasu su ka shiga hannun 'yan sanda.A zance da ake yi dai mun je ofishin 'yan sandar domin samun ƙarin bayyani sai dai sun ce yazuwa yanzu babu wani bayyani da zasu yi. Daga bisani dai na yi tattaki har zuwa a ofishin ministan kula da makarantun sakandri na ƙasa domin jin ta bakinsu,dangane da wanann zanga-zanga kuma Malam Zakari Hima Barkire daraktan kula da makarantun sakandrI na birnin Yamai ya kare kansu yana mai cewar.

''Lalle gaskiya ne mun yi alƙawari zuwa Nuwamba 15 zamu yi azzuzuka na zana kuma mun ba da kwangilar aikin a farkon watan Oktoba lokacin da damina ba ta kau ba, don haka a yanzu ba zasu iya samun ɗakunan ɗaukar darasin ba, sai sun jira kaɗan wanga lokaci ya wuce.''Yanzu haka dai tuni gwamnati ta sake komawa teburin tattaunawa da dalibban inda ake sa ran gano bakin zaren rikicin.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da hira da Suleiman Babayo ya yi da Mahaman Lokoko shugaban haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyin farar hula masu fafutukar samar da illimi a Nijar.

Mawallafi : Gazali Abdou Tassawa
Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin