Yamutsin siyasa da neman iko sun gurgunta Libiya | Labarai | DW | 21.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yamutsin siyasa da neman iko sun gurgunta Libiya

Al'ummar birnin Tripoli, ta wayi gari da jin karan fashewar man'yan makammai, da kuma harbe-harbe. inda kusan komi ya rikidewa jama'a

Da sanyin safiyar yau Laraba (21.05.2014), kusa da wasu barikokin soja guda biyu da ke Tripoli babban birnin kasar Libiya aka tashin bindigogin na fitowa, inda wadanda suka jiye ma kansu abubuwan da suka faru, suka ce, an samu musayar wuta a kewayan barakokin soja na Tadjoura da ke gabacin birnin, da kuma na Yarmouk.

Kasar Libiya dai ta shiga cikin wani hali na tsaka mai wuya, tun bayan mutuwar Mouammar Kadhafi a shekarar ta 2011, inda hukumomin da suka gaje shi suka kasa shawo kan mayakan kasar, inda kowa ke abun da yaga dama da makamman da ke hannun sa.

A ranar Lahadi ce dai da ta gabata, wasu 'yan bindiga suka kai hari a ofishin majalisar dokokin kasar, harin da Janar Khalifa Haftar wanda a halin yanzu ya zama wani sabon madugu, ya dauki alhakin kai wa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Usman Shehu Usman