Yamutsin siyasa a Bangladesh | Labarai | DW | 05.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yamutsin siyasa a Bangladesh

Al'amura sun rikiɗe a ƙasar Bangladesh, inda 'yan adawa suka yi ta ƙone-ƙone matakin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane

Masu zanga-zanga a ƙasar Bangladesh sun cinna wuta kan rumfunan zaɓe a yau Lahdi, yayinda ƙasar ke gudanar da zaɓe gama gari, wanda 'yan adawa suka ƙi shiga. Rahotanni daga Dhaka babban birnin ƙasar ta Bangladesh suka ce, an kashe aƙalla muta ne 15, a yamutsin da dubban 'yan adawa suka haddasa. 'Yan sanda sun buɗe wuta kan masu adawa, masu bore da suka cinna wa aƙalla rumfunan zaɓe dari biyu wuta, kana suka ɗauke ƙuri'a suka yaga, wasu kuma aka ƙwana. Sayed Abu Sayim shugaban 'yan sanda a arewacin ƙasar, ya ce masu adawa ɗauke da bama-bamai haɗin gida sun yi ta bin rumfa-rumfa suna ƙonawa, haka kuma suna lakaɗa wa malaman zaɓe duka, inda har suka hallaka wasu, kana suka cillawa 'yan sanda wuta da bam haɗin gida. 'Yan sandan dai sun buɗe wuta, inda suka hallaka muta ne, a wani abin da suka ƙira mataki ne na kare kai. Tun kafin zaben dai y'an adawa suka gargaɗi gwamnati, wanda suka zarga da shirya zaɓe don dorewa kan mulki.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu