Yammacin Afrika ta yi a dabo da cutar Ebola | Labarai | DW | 14.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yammacin Afrika ta yi a dabo da cutar Ebola

A ranar Alhamis din nan ce hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewar an sami nasar kakkabe kwayar cutar Ebola daga kasashen yammacin nahiyar Afrka baki daya.

Kwararru da ke cikin hukumar ta WHO, sun kuma yi gargadi cewar duk da nasarar da aka samu, to kuwa a hannu daya dole ne a cigaba da taka tsan –tsan don kaucewa sake bullar cutar ta Ebola.

Bayanin kakkabe kwayar cutar ta Ebola a yammacin Afrika ya shafe kwanaki 42 bayan tabbatar da bullar kwayar cutar ta karshe a kasar Laberiya, dake kasancewa kasa ta karshe a yammacin Afrika da cutar ta fi kamari.

Fiye da mutane sama da dubu goma sha daya ne suka mutu sakamakon bullar kwayar cutar ta Ebola a shekara ta 2013, a yayin da karin wasu sama da dubu 28 suka kamu da kwayar cutar.