1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki ya kori mutane dubu 80 daga gidajensu a Kwango

Gazali Abdou Tasawa
July 12, 2017

MDD ta ce mutane dubu 80 suka tsere daga garuruwansu a cikin kwanaki shida kadai a garin Fizi na yankin Kudancin Kivu inda ake ci gaba da gobza yaki tsakanin sojojin gwamnati da mayakan kungiyar tawayen Mai-Mai.

https://p.dw.com/p/2gP4e
Kongo französische Soldaten im Provinz Ituri
Hoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa mutane kimanin dubu 80 ne suka tsere daga garuruwansu a cikin kwanaki shida kadai a garin Fizi na yankin Kudancin Kivu da ke a Gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango inda ake ci gaba da gobza wani kazamin fada tsakanin sojojin gwamnati da kuma mayakan kungiyar tawayen Mai-Mai Yokotumba. 

A ranar 29 ga watan Yunin da ya gabata ne mayakan tawayen ta Mai-Mai suka  kwace iko da wasu garuruwa hudu a yini daya kafin daga bisani sojojin gwamnatin su fatattakesu bayan gumurzu na tsawon kwanaki biyar. 

Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Demokradiyyar kwango Maman Sidiku ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa sun damu sosai da halin da mutanen suka shiga inda suke rayuwa a cikin halin kunci a wasu sansanonin guda uku da Majalisar Dinkin Duniyar ta tanada.